Wednesday, January 15
Shadow

Amfanin bawon kankana a fuska

Ba sha a ji dadi a baki bane kadai amfanin Kankana, yana kuma da amfani masu yawa a jikin dan Adam musamman a fuska.

A wannan rubutu, zamu muku bayanin Amfanin bawon Kankana a fuska.

Bawon kankana idan aka shafashi a fuska yana sanya fuskar ta yi haske.

Hakanan kuma yana maganin abubuwan dake sa fuska ta tattare ta yi kamar ta tsaffi da kuma duhun da hasken rana ke sa fuska.

Amfani da bawon kankana ko kankanar kanta ko man shafawa da aka hada da kankana na taimakawa matuka wajan zaman fuska tana sheki irin ta matasa.

Hakanan ruwan kankana ko lemun da aka hada da kankana idan aka shafashi a fuska akai-akai, yana taimakawa wajan kawar da kurajen fuska.

Karanta Wannan  Amfanin kankana ga namiji

Shafa ruwan kankana a fuska yana kawar da tabon bakaken abubuwan dake fuska masu kama da kuraje sannan yana hana sake fitowarsu a fuskar.

Yanda ake amfani da bawon kankana wajan gyaran fuska shine, bayan samo bawon kankanar, sai a shafa cikinsa a fuska har zuwa wuya.

A barshi ya bushe sai a wanke da ruwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *