Akwai amfani da yawa da ake yi da ganyen ayaba da suka hada da dafa abinci, gasawa, dama zuba abinci a ciki a ci da kuma yin kwalliya dashi.
Ana amfani da ganyen Ayaba a matsayin kwano a zuba abinci a ciki wanda da zarar an kammala cin abincin sai a yadda. Yawancin an fi yin hakan a kasashen Asia.
Ana kuma yin amfani dashi wajan gasawa ko dafa abinci, Yarbawa kan yi amfani dashi wajan nada Alale a ciki a dafa. Sannan ana nade wasu abubuwa a ciki a gasa.
Hakanan akan yi amfani da ganyen ayaba wajan magance kaikayin fata da kuma ciwo ko bacin ciki.