Kankana na daya daga cikin kayan marmari da ake amfani dasu a kasar Hausa, a wannan rubutun, zamu kawo muku jawabin amfanin Kankana ga Namiji.
Kankana na taimakawa maza wajan lafiyar gabansu musamman maraina ga mazan da suka fara manyanta.
Tana da sinadaran Antioxidant wanda ke boye alamun tsufa.
Tana kara gudun jini a jikin mutum wanda hakan zai karawa namijin dake shanta karfin Azzakari.
Masana sunce ga maza wanda suka manyanta wanda ke amfani da maganin karfin maza dan Azzakarin su ya tashi, zasu iya yin amfani da kankana a madadin shan wadannan magunguna.
Kankana na taimakawa wajan samun ingantaccen bacci.
Kankana na taimakawa maza wajan kara ingancin maniyyinsu.
Kankana na taimakawa karin lafiya ga zuciya.
Kankana na kuma da sinadaran dake yaki da cutar Daji watau cancer.
Kankana na taimakawa wajan saukaka narkewar abinci.
Tana garkuwa ga kamuwa da cutar sarkewar numfashi.
Kankana na kara kuzari na jiki.