Monday, December 16
Shadow

Amfanin waken suya a jikin mace

Waken suya na daya daga cikin manyan abinci a kasar Hausa inda ake abubuwa dashi da yawa kama daga Awara, madara, kai wasu ma na soyashi a rika ci kamar gyada.

A wannan rubutu zamu bayyana amfanin waken suya a jikin mace.

Waken suya na da amfani sosai musamman ga mace wadda ta fara manyanta, alamomin tsufa da kuma sakin jiki ba zasu bayyana sosai ba idan tana amfani da waken suya.

Matan da suka kai matakin manyanta,sukan yi fama da zufar dare, yawan amfani da waken suya na magance wannan matsala.

Hakanan ga matan dake son rage kiba, waken suya na taimakawa sosai a wannan bangaren.

Hakanan yana taimakawa mata wajan rage matsalolin jinin al’ada.

Wani bincike yace waken suya na taimakawa wajan garkuwa ga hana kamuwa da cutar dajin mama watau Breast cancer.

Yana kuma taimakawa mata masu fama da hawan jini.

Hakanan yana taimakawa mata masu fama da ciwon suga.

Masana kiwon lafiya sunce yana da kyau kananan yara mata su rika cin waken suya sosai saboda idan sun girma yana basu kariya daga kamuwa da cutar dajin mama watau breast cancer.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *