Saturday, December 21
Shadow

Aminu Ado Bayero ba zai yi sallar Juma’a a Ƙofar Kudu ba – Ƴansanda

Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta gargaɗi al’umma su guji yaɗa ‘labaran ƙarya’ da ke cewa sarkin Kano da aka sauke Aminu Ado Bayero zai halarci sallar Juma’a a babban masallacin fadar sarki da ke Ƙofar Kudu.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da rundunar ƴansandar ta fitar yau Juma’a, wadda ta samu sa hannun mai magana da yawun rundunar a jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa.

A cewar sanarwar ya kamata al’ummar jihar su yi watsi da labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa sarkin wanda aka sauke zai halarci sallar Juma’ar a Ƙofar Kudu kasancewar ba gaskiya ba ne.

Haka nan rundunar ta tabbatar da cewa za ta samar da wadataccen tsaro faɗin jihar.

Karanta Wannan  Sarautar Kano: Duk Gwamnatin Ganduje ce ta fara kawo matsalar nan ta raba kan 'yan Uwan gidan Sarauta>>Sani Musa Danja

Ana cikin halin ɗar-ɗar a jihar ta Kano tun bayan da Aminu Ado Bayero, wanda gwamnatin jihar ta sauke ya koma birnin na Kano bayan miƙa wa Muhammadu Sanusi II takardar kama aiki a matsayin sarkin Kano na 16.

A ranar Juma’a 24 ga watan Mayu, 2024 Sarki Muhammdu Sanusi II ya karɓi takardar kama aiki a matsayin sarkin Kano na 16, kwana ɗaya bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar masarautar Kano ta 2024, wadda ta soke masarautu biyar na jihar.

A shekarar 2019 ne majalisar dokokin jihar Kano ta yi dokar da ta samar da masarautun Kano, Rano, Bichi, Gaya da kuma Ƙaraye, sannan kuma daga bisani gwamnatin jihar ta sauke Muhammadu Sanusi II a msatyin sarkin Kano na 14 bayan zargin shi da rashin biyayya da kuma almundahana da kuɗi.

Karanta Wannan  Ƴansanda sun kori ƴandaba da mafarauta daga fadar Kano,ji dalili

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *