Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ana bukatar hanyar sasanci domin kawo karshen yakin yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da daidaita lamurra a kan iyakar arewacin Lebanon.
Mista Biden ya ce akwai bukatar shugabannin Falasdinawa da na Isra’ila su hada kai domin sake gina Gaza, ta yadda ba za a bar Hamas ta sake mallakar makamai ba.
”Amurka za ta tallafa wajen sake gina makarantu da asibitocin Gaza”, in ji Biden.
Ya kara da cewa shirin zai taimaka wajen sake daidaita lamurran dangataka da Saudiyya da magance barazanar Iran a yankin.
Mista Biden ya kuma gabatar da kudurin da zai bai wa Isra’ila damar zama mai karfi a yankin.