
Wata kungiya me suna Quartus Economics ta bada shawara ga babban bankin Najeriya da ya fito da takardar kudin Naira 20,000 da 10,000.
Kungiyar tace dalili kuwa shine a yanzu takarar Naira 1000 bata iya sayen wani abin a zo a gani.
Tace fito da manyan kudaden zai ragewa mutane wahalar daukar kudade da yawa wajan gudanar da kasuwanci.
Ungiyar tace ba gaskiya bane abinda ake fada cewa idan aka fito da sabbin kudin zasu iya saka farashin kayan masarufi su tashi.
Kungiyar tace darajar Naira ta lalace sosai.