
Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya da hadin gwiwar wasu kamfanoni masu zaman kansu, sun baiwa kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles Kyautar dala $30,000 akan kowace kwallo daya da suka ci, kamar yanda hukumar ta yi Alkawari.
An basu wadannan kudaden a dakin canja kaya bayan kammala wasan.
Kudin zasu kama jimullar Dala $120,000 kenan tunda kwallaye 4 ‘yan kwallon suka ci Gabon jiya.