Friday, July 17
Shadow

An bayyana yawan kudin da aka baiwa kowane dan fim da ya je Abuja murnar ranar zagayowar Dimokradiyya

Zuwan taurarin fina-finan Hausa wajan bikin ranar Dimokradiyya ta kasa Abuja ya bar baya da kura.

Da yawa sun rika sukar ‘yan fim din da fadin cewa bai kamata ba abinda suka yi musamman yayin da takwarorinsu na kudu ke zanga-zanga da nuna damuwa kan harkar matsalar tsaron Najeriya.

Dan Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa, abinda aka baiwa ‘yan fim din bai wuce Naira 150,000 ba kowanne wanda yace ba kudin yanke talauci bane.

Yace idan basu fito suka yi zanga-zanga ba, bai kamata a gansu suna murna ba.

Karanta Wannan  A Wasu Lokutan Yawan Roko Ne Ke Hana Wasun Mu Shiga Cikin Jama'a Idan Mun Dawo Gida Yin Hutu Daga Turai, Cewar Dan Kwallon Nijeriya, Sadiq Umar Wanda Ke Wasa A Kungiyar Valancia Dake Kasar Sifaniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *