Thursday, November 19
Shadow

An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin India da Pakistan

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Indiya da Pakistan sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta nan take.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce: “Bayan tattaunawa ta tsawon dare da Amurka ta shiga tsakani, ina farin cikin sanar da cewa Indiya da Pakistan sun amince da tsagaita wuta nan take.

“Ina yi wa duka ƙasashen murna saboda amfani da hankali wajen amincewa da tsagaita wuta,” in ji Trump.

Karanta Wannan  Har yanzu bamu san dalilin da yasa, Abba ya koma APC ba>Inji Kwankwaso

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *