Hukumomi a kasar Maldives sun dakatar da ministar Muhalli ta kasar, Fathimath Shamnaz Ali Saleem bisa zargin tawa shugaban kasar, Mohamed Muizzu sihiri wanda yasa yake ta lalata da ita ba tare da ya sani ba.
An dai dakatar da ita daga aikin ministar tare da wasu 2 inda hukumomi a kasar ke cewa suna bincike akanta.
Zuwa yanzu dai hukumomin kasar basu bayyana irin sihirin da Fatima tawa shugaban kasar ba.
Amma wasu rahotanni da ba’a tabbatar dasu ba sun bayyana cewa, Fatima ta yi lalata da shugaban kasar ne wanda daga baya matar shugaban kasar ta gano.
Dan hakane mataar shugaban kasar ta sakata gaba, inda ta yi sanadiyyar kulla mata abinda yasa aka kamata.
Wasu majiyoyi sun kara da cewa, ana zargin Fatima ta sihirce Shugaban kasar ne.