
An dakatar da wasanni guda huɗu na gasar Serie A ta ƙasari Italiya bisa rasuwar Fafaroma Francis.
A ranar Litinin fadar Vatican ta sanar da rasuwar fafaroman wanda ya shafe shekara 88 a duniya bayan wata jinya da ya yi har aka kwantar da shi a asibiti.
Karawar da aka soke ta haɗa da:Torino v Udinese, Cagliari v Fiorentina, Genoa v Lazio and Parma v Juventus.
Hukumar da ke lura da gasar ta Serie A a ƙasar ta ce za ta duba wani lokacin da za a buga wasannin a nan gaba.
Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da dama sun miƙa ta’aziyyar su bisa rasuwar shugaban cocin katolikan na duniya.