Friday, December 5
Shadow

An daure likitan Najeriya a gidan yari saboda sumbatar mara lafiya har sau biyu ba tare da son ranta ba

Wani likita dan Najeriya dake aiki a kasar Ingila an daukeshi tsawon shekara daya saboda sumbatar wata mata marar lafiya dake karkashin kulawarsa.

Likitan me suna Adewale Kudabo ya fara sumbatar marar lafiyar ne a lebenta yayin da take kwance bata iya motsi sannan ya sake sumbatar ya a karo na biyu.

Lamarin ya farune a Asibitin York Hospital.

Saidai likitan yace ba da wata manufa yayi hakan ba yana son nuna jin kai ne ga marar lafiyar kuma ba a lebenta ya sumbaceta ba, ya sumbaceta ne goshi.

Marar lafiyar ta gayawa kotu cewa, sam bata ji dadin abinda ya mata ba ya sakata a fargaba da tsoro da damuwa.

Karanta Wannan  Lauya ya garzaya kotu inda yake neman ta hana Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan tsayawa takarar shugaban kasa a 2027

Lauyan wanda akw zargi yace sun amsa laifin wanda ake zargin amma suna neman sauki saboda wannan ne karin farko da ya aikata wannan laifi.

Mai shari’a Alex Menary yace ya gamsu da hujjojin cewa a baki yawa marar lafiyar sumbata ba a goshi ba kuma hakan cin amanar aikinsa ne dan haka ya daureshi tsawon shekara daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *