
Babbar kotun jihar Ekiti ta sanar da hukuncin daurin shekaru 44 ga wasu malamai da aka kama da laifin yiwa dalibansu fyade.
Malaman sune Ajibola Gbenga dan shekaru 43 sai kuma Olaofe Ayodele dan shekaru 52.
Daya daga cikin yaran da sukawa fyaden me shekaru 17 ta bayyana cewa akwai ranar da daga makaranta ya bata kudi naira 200 yace ta je gaban wani gidan mai ta jirashi.
Tace tana tsaye sai ga wata dalibar itama ta je wajan inda tace malamin nasu ne itama yace ta jirashi a wajan
Tace suna tsaye sai malamin nasu ya karaso shi da abokinsa ya tafi dasu zuwa wani Otal. Inda anan ne aka kaisu dakuna daban-daban aka yi lalata dasu.
Tace daga nan sai malamin ya rika damunta da yawa.
Daga nan ta ce sai ta fara sanarwa da mahaifiyarta saboda abin ya dameta.
Lauyan yaran ya kira shaidu 4 wanda suka bayar da shaida sannan kuma ya gabatar da takardar asibiti wadda ta tabbatat da zargin.
Saidai wadanda ake zargin duk sun musanta zarge-zargen da akw musu inda suma suka kira shaidunsu amma alkalin yace ya gamsu da shaidar yaran da akawa fyaden.
Sannan ya yanke musu hukuncin daurin shekaru 22 a gidan yari kowannensu ba tare da damar biyan Haraji ba.