Wani sabon rahoto da jaridar Punch ta yi ya bayyana cewa, Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na biyan Tallafin man fetur.
Hakanan akwai tanadin biyan tallafin ma har na Naira Biliyan 5.4 da za’a biya nan da karshen shekarar da muke ciki.
Hakan na kunshene a cikin wani daftarin kokarin fitar da Najeriya daga matsin tattalin arzikin da take fama dashi.
Daftarin ya kunshi baiwa mutane da yawa ‘yan Najeriya kudin tallafi da kuma kawo saukin farashin kayan masarufi da sauransu.
Rahoton yace gwamnati ta kasa cire tallafin man fetur din gaba daya lura da yanda a yanzu haka ake tsaka da matsin tattalin arziki me tsanani.
Wannan daftari za’a yi amfani dashi ne cikin watanni 6 masu zuwa.
Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu dai ta na ta ikirarin cewa ta cire tallafin man fetur amma masana na cewa har yanzu ana biyan tallafin.