
An gudanar da taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a Abuja.
An gudanar da taronne a gidan Gwamnatin jihar Bauchi dake Asokoro A Abuja.
Manyan ‘yan jam’iyyar da yawa da suka hada da Ahmad Makarfi, Seriake Dickson, Gwamna Bala Muhammad, Gwamna Agbu Kefas, Gwamna Ahmadu Fintiri, Gwamna Dauda Lawal Dare, Gwamna Ademola Adeleke, Gwamna Caleb Muftwang, Da Dai Sauransu.
Wani abin ba zata shine, Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ma ya halarci taron