Saturday, June 27
Shadow

Ban damu sai na koma Kujerar Gwamna ko ta halin kaka ba>>Gwamnan Jihar Rivers Simi Fubara

Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara ya bayyana cewa, bai damu sai ya koma mukaminsa na gwamna ba ko ta halin kaka.

Ya bayyana hakanne a wajan wani taron tunawa da dattijon jihar, Marigayi, Edwin Clark, inda masu jawabi da yawa da auka tashi suka soki dakatar dashi da aka yi da neman a mayar dashi kujerar Gwamna.

Fubara da ya hau wajan jawabi ya nesanta kansa da kalaman mutanen inda yace bai kamata a yi fito na fito kan lamarin ba.

Ya kara da cewa, suka san ko yana son komawa Kujerar gwamnan? Yace shi a yanzu ma ruhinsa ya bar gidan Gwamnatin jihar.

Karanta Wannan  Hukumar Kula da jami'o'in Najeriya, NUC tace wadanda aka baiwa Digirin Girmamawa irin wadda aka baiwa Rarara su daina Amfani da sunan "Dr." A jikin sunansu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *