Rahotannin da muke samu daga kasar Nijar na cewa hukumomi a kasar sun sanar da haramta jin wakokin mawakin siyasa Dauda Kahutu, Rarara.
Hakan na zuwane bayan da Rarara yawa shugaban kasar Nijar Tchadi Barazanar ya dawo da Bazoum kan mulki ko kuma ya fara zubo masa wakoki.
Rarara yace “Na bawa Tchani kwana 20 ya dawo da Bazoum ko ya sanya lokacin zabe, ko kuma na soma zubo masa wakoki ba kakkautawa”
A sanarwar da kafar Damagaram Post ta ruwaito tace ne kawai an haramta jin wakokin Rarara din a Jamhuriyar Nijar amma basu bayar da cikakken bayani ba.