Rahotanni sun bayyana cewa, ranar Litinin an ji karar harbin bindiga a kusa da karamar fadar sarkin Kano dake Nasarawa.
A nan ne dai Sarki Aminu Ado Bayero yake zaune inda ya kafa fadarsa bayan da aka saukeshi daga sarautar Kano.
Rahoton Premium Times yace an yi harbinne dan hana kama Aminu Ado Bayero wanda kotu ta bayar da umarnin fitar dashi daga fadar ranar Litinin.
Wannan harbi da aka yi yasa mutane suka rika canja hanya suna komawa da baya.
Rahoton yace ba’a tabbatar da ko jami’an tsaro ne ko masu tsaron fadar bane suka yi harbinba.