Hadimar gwamnan jihar Kaduna dake bashi shawara akan harkokin siyasa, Hon. Rachael Averik ta tsallake rijiya da baya a yunkurin kisheta da aka yi.
An kaiwa tawagar Hon. Rachael Averik harin kwantan baunane ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu.
Harin ya farune a tsakanin kauyukan Tsauni Majidadi da Gani dake karamar hukumar Sanga ta jihar.
A ranar tana kan hanyar zuwa Gwantu ne abin ya faru.
A ranar taje gaisuwane sannan ta kaddamar da Asibitin da Alhaji Muhammad Umar Numbu ya gina a masarautar Arak.
Jami’an tsaron dake tare da ita sun budewa maharan wuta inda anan aka jikkata direbanta da Dansanda daya.
Jami’an tsaro a jihar sun fara bincike kan lamarin.
Gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da harin.