Wani boka me suna Timothy Dauda dan kimanin shekaru 19 a jihar Edo da yayi ikirarin yana da maganin Bindiga ya shiga hannu.
An kamashine bayan da ya gwada maganin Bindigar akan wani amma maganin bai yi amfani ba,Bindigar ta kamashi ya mutu.
Lamarin ya farune a yankin Onumu dake karamar hukumar Àkókò-Edo A jihar ta Edo
Kakakin ‘yansandan jihar SP Moses Joel Yamu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace wanda ake zargi zai fuskanci hukunci.