Wata malamar Makaranta ta shiga hannun hukuma bayan data daki dalibarta me shekaru 3 saboda ta kasa rubuta lamba 6.
Lamarin ya farune a makarantar Christ-Mitots School dake Ikorodu, Legas.
Bidiyo ya bayyana yanda malamar ta rika dukan dalibartata Abayomi Micheal me shekaru 3.
Hakan ya jawo Allah wadai wanda yayi sanadiyyar kama malamar.
Tuni Hukumar ‘yansandan Najeriya ta tabbatar da kama matar inda sukace za’a tabbatar da an yi adalci wajan hukuntata.