Tuesday, May 19
Shadow

Ban taba ganin mutane a cikin yunwa me tsanani ba irin a mulkin Tinubu>>Inji Omoyele Sowore

Dan gwagwarmaya kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya bayyana cewa bai taba ganin mutane a cikin tsananin yunwa irin ta zamanin mulkin Tinubu ba.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Sahara Reporters.

Yace Gwamnatin Tinubu ta yi alkawarin idan ta cire tallafin man fetur, zata yi amfani da kudin wajan gina kasa da ayyukan ci gaba.

yace bai dade da dawowa daga jiharsa ta Asaliba, jihar Ondo amma bai ga wani abin ci gaba ba da aka gina. Yace rabon da ya ga lalataccen titi irin wanda ya gani an dade.

Karanta Wannan  An gayyaci Sanata Shehu Sani ya shiga cikin wadanda zasu yi Alkalancin budurwar da zata lashe sarauniyar kyau a Najeriya amma yace baya so dan ko tsakanin matansa bai iya yin alkalancin wadda tafi kyau ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *