‘Yansanda a jihar Adamawa sun kama wani matashi me suna Ali Yaro dan kimanin shekaru 19 bayan da ya kashe dansa me kwanaki 3 kacal a Duniya.
Da aka tambayeshi dalili ya bayyana cewa talauci ne da matsin rayuwa ya jefashi yin wannan aika-aika.
Ya kwaci danne daga hannun masoyiyarsa me suna Safiya inda ya tafi dashi ya kasheshi ya binne gawar.
Lamarin ya farune ranar 7 ga watan Nuwamba, a karin Kwacham dake karamar hukumar Mubi ta Arewa.
Budurwar tasa ce dai ta matsa masa akan ya rika kula da ita da dan nata inda a sanadiyyar hakane yasa har ya karbi dan ya kasheshi.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Suleiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace wanda ake zargin ya amsa laifinsa da cewa shine ya kashe yaron.