Monday, December 9
Shadow

An kama matashi dan shekaru 19 da ya kàshè dansa me kwana 3 a jihar Adamawa

‘Yansanda a jihar Adamawa sun kama wani matashi me suna Ali Yaro dan kimanin shekaru 19 bayan da ya kashe dansa me kwanaki 3 kacal a Duniya.

Da aka tambayeshi dalili ya bayyana cewa talauci ne da matsin rayuwa ya jefashi yin wannan aika-aika.

Ya kwaci danne daga hannun masoyiyarsa me suna Safiya inda ya tafi dashi ya kasheshi ya binne gawar.

Lamarin ya farune ranar 7 ga watan Nuwamba, a karin Kwacham dake karamar hukumar Mubi ta Arewa.

Budurwar tasa ce dai ta matsa masa akan ya rika kula da ita da dan nata inda a sanadiyyar hakane yasa har ya karbi dan ya kasheshi.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: Jami'in Tsaron Gidan yari ya kashe abokin aikinsa saboda abinci a jihar Bauchi

Kakakin ‘yansandan jihar, SP Suleiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace wanda ake zargin ya amsa laifinsa da cewa shine ya kashe yaron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *