‘
Yansanda a jihar Ogun sun kama wani matashi me suna Muniru Haruna dan kimanin shekaru 25 bisa zargin yiwa yarinya me shekaru 3 fyade a ranar 1 ga watan Ramadana.

Lamarin ya farune a Orile-Ilugun dake karamar hukumar Odeda ta jihar Ogun.
Kakakin ‘yansandan jihar, CSP Omolola Odutola ya tabbatar da faruwar lamarin.
Yace mahaifiyar yarinyar, Alaba Abdullahi me shekaru 20 ce da kanta ta kai karar wanda ake zargi da misalin karfe 11 na safiyar ranar Asabar, 1 ga watan Maris wadda ta yi daidai ga 1 ga watan Ramadana.
Tace suna zaune a gida daya da matashin inda tace yarinyar na wasane kamin matashin ya zakke mata, tace ta ji kukan diyarta inda ta fito bata iya tafiya kuma tana cikin firgici.
Hakan yasa ta kira dauki inda aka kama wanda ake zargin, an garzaya da yarinyar zuwa asibiti inda ake jiran sakamakon binciken da likitoci suka gudanar.
Shi kuma wanda ake zargin an tsareshi saidai ya musanta zargin da ake masa.