Mahukunta a garin Kwantagora dake jihar Naija sun kama wani me garkuwa da mutane.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da kamen a karshen makon da ya gabata, yace wanda ake zargin, Nasiru Isyaka na tare da wasu gungun masu garkuwa da mutanene da suka kai hari kauyen Sabon-Gari Mangu Matachibu inda suka kashe mutum daya da yin garkuwa da wasu biyu.
Nasiru Isyaka dai shima dan garin Sabon-Gari Mangu Matachibu kuma bayan da aka kubutar da wadanda suka yi garkuwa dasu, ya je yi masa jaje inda a nan ne ya ganeshi.
Ya kara da cewa an kwace bindiga hadin gida guda daya daga hannunsa sannan kuma ya amsa laifin da ake zarginsa dashi.