
‘Yansanda a jihar Yobe sun kama mutane 2 da ake zargin sun yiwa yarinya me shekaru 12 fyade a jihar.
Lamarin ya farune a kauyen Jalingo dake karamar hukumar Tarmuwa ta jihar.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwar lamarin a Damaturu ranar Litinin.
Ya kara da cewa lamarin ya farune ranar 15 ga watan Fabrairu da misalin karfe 3:30 na rana inda wanda ake zargin suka ja yarinyar zuwa daji suka zakke mata.
Ya kara da cewa, sun jiwa yarinyar ciwo inda aka kai ta Asibiti sannan kuma an kama wadanda ake zargin.