
Hukumar ‘yansanda ta jihar Naija ta sanar da kama mutane 3 bisa zargin siyan ciki wata 6 dan yin amfani dashi wajan tsafi.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace wadanda ake zargin sun baiwa matar Naira Miliyan 30 dan ta yadda su cire cikin nata.
Yace a ranar 17 ga watan Fabrairu ne suka kama mutanen masu sunan Martha Andrew, James Luka da Johnson John wadanda duka sun fito ne daga Minna.
Yace an kamasu ne a yayin da suke kokarin daukar matar me ciki daga garin Rafin-Yashi zuwa ga wani mutum me suna Gbege, saidai mutumin tuni ya tsere.
Yace an kama mutanen ne a wani Otal dake Minna kuma duka sun amsa laifukansu sannan a yanzu ana kan kokarin kama Gbege wanda ya tsere.