‘
Yan sanda a jihar Naija sun kama soja, Private Sadiq Sani bisa zargin aikata Fashi da makami.

An kamashi kuma da zargin cin zaafin wani dan kasuwa me suna Abdulrahman Salihu.
Rahoton yace, Soja Sadiq ya je shagon Abdulrahman Salihu da sallah inda ya sayi kaya, sai yace a bashi account Number ya tura kudi.
Saidai bayan da ya karbi account number din dan kasuwar yayi zargin wani abu inda yace ba zai bashi kayan ba sai ya ga Alert.
Daga nan ne sai sojan ya aika da alert din karya.
Ko da dan kasuwar ya ga haka sai rikici ya barke tsakaninsu inda sojan ya fitar da wuka ya yanki dan kasuwar sannan ya tsere.
An sanar da ‘yansanda inda suka bi sojan har gidansa dake Limawa a garin Minna suka kamashi.
An kaiwa hukumar soji rahoton abinda sojan ya aikata inda wani babban soja me suna Captain U.S Ibrahim ya karbi lamarin da bada tabbacin yin bincike da aikawa da sojan Hedikwatar tsaro dake Abuja.