
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Kabir Gombe ya bayyana irin Arzikin da Allah ya masa.
Malam ya bayyana hakane a wani bidiyo da ya bayyana inda aka ganshi yana wa’azi.
Yace riguna da suke ta dinkawa, inda za’a tarasu babu dakin da zai daukesu, yace amma ba ba konawa suke ba, bayarwa suke yi ga bayin Allah inda yace a shekara yakan yo kyauta da riguna 100.
Kalli Bidiyon anan:
Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da Dan Bello ya fitar da bayanai kan zargin shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau da aikata ba daidai ba da dukiyar gina azuzuwa.