An Kama wani Ɗan Nijar a Dajin Yankari sanye da kayan sojoji.

Rundunar ‘yan sandan Bauchi ta kama wani mutum mai suna Jibrin Ali, ɗan shekara 28 daga Zandar, Jamhuriyar Nijar, a cikin dajin Yankari da ke ƙaramar hukumar Alkaleri. An kama shi ne yayin sintiri na hadin gwiwa, yana sanye da kayan sojoji, kuma ana zargin yana ciki waɗanda suke tada hankali a yankin wanda ya ke fama da ayyukan ‘yan bindiga, ya kasa bayar da sahihin bayani kan dalilin kasancewarsa a dajin.
Kwamishinan ‘yan sanda ya bada umarnin a gudanar da cikakken bincike.