
Kusan duka manyan jagorin Adawa na jam’iyyar ADC sun bayyana cewa idan aka basu damar tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar, wa’adi daya zasu yi.
Rahotanni sun ce tuni Peter Obi ya mikawa tawagar ‘yan adawar alkawarin wa’adin mulki daya zai yi idan aka zabeshi.
Hakanan shima Rotimi Amaechi ya bayyana bukatar a bashi takarar shugaban kasa a jam’iyyar inda yace wa’adi daya zai yi ya sauka, ya kuma ce dan kudu ne ya kamata ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar a 2027.
Hakanan kuma Shima Atiku ya taba fadar cewa idan ya hau mulki, wa’adi daya zai yi ya sauka.
Wannan bukata da duka su 3 din suke da ita a tsakaninsu na iya zama barazana ga hadin kan jam’iyyar, kamar yanda masana suka bayyana.