Friday, December 5
Shadow

An kama wasu dake amfani da lokacin aikin Hajji suna kai Miyagun Kwàyòyì kasar Saudiyya

Hukumar hana sha da fataucin Miyagun Kwàyòyì ta NDLEA ta sanar da kama wasu dake amfani da lokacin aikin Hajji suna safarar miyagun Kwàyòyì zuwa kasar Saudiyya.

Hakanan, Rahoton yace kuma suna daukar nauyin mutane zuwa kasar Saudiyyar kawai dan su yi musu safarar kwaya.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemine ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar ranar Lahadi inda yace sun yi nasarar kama shugaban wannan muguwar harkar a Kano.

Yace wadanda aka kama din sune Abubakar Muhammad, Abdulhakeem Muhammed Tijjani, da Muhammad Aji Shugaba.

Yace an kamasu ne ranar 27 da 28 ga watan Mayu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Soja Boy ya sakw yin waka da Tsohuwar me saka Hijabi, Iftihal Madaki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *