
Wata mata a kasar Thailand na fuskantar tuhumar jan hankalin malaman Buddha suka yi Alfasha da ita sannan ta kuma rika karbar kudi a hannunsu inda tace ko dai su rika bata kudi ko ta tona musu asiri.
Wannan abun da malaman suka aikata ya sabawa ka’idar Buddha wanda yace malamai basa aure kuma basa neman mata.
Malamai 9 ne aka samu da wannan aika-aika inda duka an koresu.
Sunan matar da ta yi wannan abu Wilawan Emsawat kuma tana tsakanin shekaru 30 ne, an ce daya daga cikin malaman ya rika dibar kudin wajan ibadarsu yana aika mata.