Wednesday, January 15
Shadow

An kashe jimullar Mutane 4,416 sannan an yi garkuwa da 4,334 a shekara 1 da Tinubu yayi yana mulkin Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa, an kashe jimullar mutane 4,416 da yin garkuwa da guda 4,334 a shekara 1 da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi yana mulki.

Wata gamayyar masu fafutukar kasa da kasa da kuma Najeriya su 84 ne suka fitar da wannan rahoto.

Rahoton yace kungiyoyin basu saka abubuwan dake faruwa na fashi da makami da sauran laifuka ba.

Sunce wannan lamari ya sanya ‘yan Najeriya sun rasa ‘yancin rayuwa me inganci da kuma rayuwa cikin walwala.

Kungiyar tace ci gaba da wannan lamari ya jefawa ‘yan Najeriya tsoro da fargaba da rashin tabbas.

Kuma sun ce idan gwamnatin Tinubu bata dauki mataki kan lamarin ba, suna daf da fitar da rahoton yanke tsammani akanta.

Karanta Wannan  Ji yanda ake ciki kan maganar mafi karancin Albashi tsakanin Gwamnati da NLC, inda ake tunanin za'a sake komawa yajin aiki

Sunce suna jawo hankalin gwamnatin Tinubu data yi kokari wajan sauke nauyin dake kanta na kare rayuwa da dukiyar ‘yan kasa kamar yanda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *