
Jami’ar ATBU dake Bauchi ta sallami daya daga cikin malamanta me suna Dr. Usman Mohammed Aliyu bisa zargin neman yin lalata da dalibarsa wadda matar aurece.
Dalibar me suna Kamila Rufa’i Aliyu ta zargi malamin da cewa ya aika mata sakonnin batsa sannan ya nemi yayi lalata da ita.
Data kiya, sai ya ce zai kayar da ita jarabawa duk da cewa yasan ita matar aurece.
Saidai Dr. Usman ya shigar da kara kotu inda yake neman hakkinsa saboda a cewarsa, Kamila ta bata masa suna.
Mijin Kamila, Ja’afaru Buba ta hannun lauyansa ya shigar da karan makarantar inda ya bayar da dukkan hujjojin da yake dasu na cewa Dr. Usman ya nemi yin lalata da matarsa.
Bayan kammala bincike, Hukumar gudanarwar jami’ar ta ce ta samu Dr. Usman da laifi inda tace ta sallameshi daga aiki.
Sannan ya mika duk wani abu mallakin makarantar dake hannunsa.