
Wani tsohon Ma’aikacin Gwamnati me suna Muhammad Zakari ya koka da cewa, wasu abokai sun yadashi basu ma daukar wayarsa shekara daya bayan da ya ajiye aiki.
Yace ya fuskanci kalubale da yawa bayan ajiye aikin kuma wannan na daya daga cikinsu.
Saidai yace hakan ya koya masa darasin cewa Yana da kyau mutum ya kulla alaka da mutane ba na wajan aikinsa kadai ba.
Muhammad Zakari ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook.