
Rahotanni daga jihar Katsina na cewa, jami’an tsaro sun kubutar da daya daga cikin dalibai 4 da aka yi garkuwa dasu daga jami’ar FUDMA dake Dutsimma jihar Katsina.
Hakanan rahoton yace ana kan kokarin kubutar da sauran dalibai 3 din da suka rage a hannun masu garkuwa da mutanen.
Dalibin da aka kubutar shine Fahad Muhammad me shekaru 20 dake tsangayar kimiyyar Kwamfuta aji daya.
Kuma an kubutar dashine ranar lahadi bayan bin sahun ‘yan Bindigar.
Sauran daliban da suka rage sune Adewale Bolaji Ajayi, 23, Emmanuel Michael, 24, da Favour Michael, 22.
Dukansu daliban suna ajinsu na farko ne a jami’ar.