Monday, July 20
Shadow

An kubutar da daya daga cikin daliban da aka yi gàrkùwà dasu a jami’ar FUDMA jihar Katsina

Rahotanni daga jihar Katsina na cewa, jami’an tsaro sun kubutar da daya daga cikin dalibai 4 da aka yi garkuwa dasu daga jami’ar FUDMA dake Dutsimma jihar Katsina.

Hakanan rahoton yace ana kan kokarin kubutar da sauran dalibai 3 din da suka rage a hannun masu garkuwa da mutanen.

Dalibin da aka kubutar shine Fahad Muhammad me shekaru 20 dake tsangayar kimiyyar Kwamfuta aji daya.

Kuma an kubutar dashine ranar lahadi bayan bin sahun ‘yan Bindigar.

Sauran daliban da suka rage sune Adewale Bolaji Ajayi, 23, Emmanuel Michael, 24, da Favour Michael, 22.

Dukansu daliban suna ajinsu na farko ne a jami’ar.

Karanta Wannan  Ban fadi zabeba, Magudi aka yi, Abin dariyane ka rasa abinda zaka yi akan wahalar da ka saka mutane a ciki saidai kace a yi addu'a>>Atiku ya mayarwa Tinubu Martani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *