Hukumar ‘yansanda a jihar Anambra ta sanar da kubutar da wasu yara 4 da aka sato daga jihar Bauchi aka kaisu Anambra aka sayar dasu ga wasu iyalai.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Obono Itam ne ya bayyana haka inda yace sun kama mutane 4 da ake zargi da hannu a lamarin.
Ya hayyana hakane ranar Litinin, 6 ga watan Janairu inda yake bayani game da yanda hukumar tasa ta gudanar da ayyukanta a shekarar 2024.
Yace daya daga cikin yaran an ganeshi kuma dukansu za’a mayar dasu ga iyayensu.
Ya kara da cewa, wadanda ake zargin sun amsa laifukansu.