Wani mutum da ya je rabon fada a jihar Adamawa an nausheshi ya mutu.
Mutumin me suna Markus Dali ya shiga tsakanin Barka Yama da Alex Tari dake fada suna naushin juna da niyyar ya rabasu.
A nan ne Barka Yarma ya nausheshi wanda shine yayi sanadiyyar mutuwarsa.
Lamarin ya farune a kauyen Sina Kwande dake karamar hukumar Michika ta jihar Adamawan.
Tuni dai aka kama Barka aka kuma gurfanar dashi a gaban kotun Magistrate dake Yola.
Wanda ake zargi dai ya amsa laifinsa inda aka kaishi gidan yari.
Kotun ta mika maganar wajan hukumar bayar da shawara kan irin lamurran dan sanin hukuncin da ya dace dashi.