
Rahotanni daga hukumar kula da harkar man fetur a Najeriya, watau Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission, sun ce an sace jimullar danyen man fetur na Naira Tiriliyan N8.41tn.
Rahoton yace an yi wannan gagarumar satar ne a tsakanin shekarun 2021 da 2025.
Saidai rahoton yace a yanzu an samu raguwar satar danyen man ba irin a baya ba amma duk da haka jimullar yawan danyen man da aka sace ya nuna gazawar gwammati.
Me sharhi akan Almuran yau da kullun, Professor Ayoade yace abin takaici ne ace an tafka irin wannan asarar amma babu wanda aka hukunta.