
Shugabar hukumar tsaron Homeland Security ta kasar Amurka, Kristi Noem ta gamu da ‘yan sane inda suka sace mata karamar jaka ta mata da ake cewa Purse.
Jakar dai na dauke da Dala $3000 da kuma katinta na aiki.
Hakanan an sace jakar ne a wani wajen cin abinci dake baban birnin kasar watau Washington DC.
Hakana Barawon ya kuma sace jakar dake dauke da magungunan matar.
Ta je gidan abincinne dan cin abinci da danginta a matsayin ranar Bikin Easter.