Friday, December 5
Shadow

An sace wayar Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa, an sace wayar Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar.

Lamarin ya farune ranar Alhamis kamar yanda kafar Leadership ta ruwaito inda tace an sace wayar Kwamishinan, Hon. Barrister Sule Shu’aibu (SAN). Ne a wajan wani taro da ya halarta.

Zuwa yanzu dai ba’a bayyana sunan barawon da yayi satar ba.

Lamarin ya baiwa mutane mamaki ganin cewa a ko da yaushe Kwamishinan na tare da jami’an tsaro ko ta yaya har barawon ya samu damar sace masa waya?

Har yanzu hukumomi a jihar Kaduna basu fitar da sanarwa kan lamarin ba.

Karanta Wannan  Shekarar mu daya cur bamu ci nama ko kifi ba, babu abinci me gida jiki babu kulawar Lafiya>>Inji Masu Laifi dake daure a gidan gyara hali

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *