
Karin ‘Yan majalisar jihar Rivers 2 sun janye daga yunkurin tsige gwamnan jihar, Simi Fubara.
‘yan majalisar, Barile Nwakoh da Emilia Amadi sun bayyana cewa sun janye daga wannan shirine bayan da wasu manya suka saka baki.
Sun bayyana cewa zai fi kyau a warware matsalar ta hanyar amfani da hanyar Sulhu.
Hakan na zuwane kasa da awanni 24 bayan da wasu ‘yan majalisar 2 suma suka janye daga yunkurin tsige gwamna Fubara.
Yanzu dai ‘yan majalisa 4 kenan suka janye daga yunk na tsige gwamna Fubara.

