
Rahotanni daga birnin New York City dake kasar Amurka yace an tsinci jaririya sabuwar haihuwa a birnin da ake zargin mahaifiyartace ta yadda ta.
An tsinci jaririyar ne a matattaqalar shiga tashar jirgin kasa ta karkashin kasa an nannadeta da tawul a Midtown Manhattan da misalin karfe 9:30 na safe.
Tuni ‘yansanda suka je suka dauketa aka kaita Asibiti inda likitoci suka tabbatar tana cikin koshin Lafiya.