Monday, April 6
Shadow

An zargi Bukola Saraki da Munafurci inda yake nuna yana PDP amma yana zagayawa ya ga Shugaba Tinubu

Jam’iyyar APC a jihar Kwara ta zargi tsohon kakakin majalisar Dattijai, Bukola Saraki da cewa, yana Adawa a jihar Ta Kwara amma yana zagayawa ya rika ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Me magana da yawun jam’iyyar APC na jihar Kwara, Abdulwaheed Babatunde ne ya bayyana hakan, inda yace ya kamata Bukola Saraki ya fito ya gayawa mabiyansa bangaren da yake.

Yace a Kwara sai ya nuna shi dan PDP ne amma sai ya rika zuwa Abuja yana ganawa da shugaba Tinubu.

Karanta Wannan  Nasan Gyare-Gyaren da nake sun jefa 'yan Najeriya a wahala amma nan gaba za'a ga alfanunsu, Ku dauka kamar maganine me daci, idan za'a sha ba dadi amma ana samun waraka>>Shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *