Wednesday, January 8
Shadow

Ana barazana ga rayuwata – Obi

Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce ana yi wa rayuwarsa barazana saboda sukar gwmnatin Shugaban Ƙasa Tinubu da ya yi a saƙonsa na sabuwar shekara.

A saƙon nasa na sabuwar shekarar, Obi ya bayyana cewa Najeriya na fama da taɓarɓarewar tattalin arziki da rashin tsaro da rashin ingantaccen kiwon lafiya.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya ce, “shin na wuce iyaka? na yi wannan tambayar ce saboda ana yi wa rayuwata da ta iyalina barazana saboda jawabin da na yi na sabuwar shekara. Bayan barazanar kuma, wani mai suna Mr Felix Morka ya zarge ni da wuce iyaka, sannan ya yi barazanar zan ɗanɗana kuɗata,” in ji shi.

Karanta Wannan  Nabil Shinkafi Ya Zama Shugaban Matasan Arewa

Obi ya ƙara da cewa idan har da gaske ya karya doka, a nuna masa, inda ya ƙara da cewa, “amma ba zan daina faɗin gaskiya ba, musamman a wannan lokacin da ƙasarmu ke ƙara shida cikin ruɗu.”

Kauce wa Twitter

Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Karanta Wannan  Tinubu ya bai wa jihohi naira biliyan 108bn kan ambaliya da zaizayar ƙasa - Shettima

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *