Wednesday, January 15
Shadow

‘Ana samun ƙaruwar bautar da ƙananan yara a Najeriya’

Wasu alƙaluman hukumomin kare haƙƙin dan adam a duniya sun nuna cewa ana samun ƙaruwar cin zarafin ƙananan yara a wasu ƙasashen duniya musamman na Afrika, ta hanyar bautar da su, ko sanya su aikin wahala.

Bayanai sun nuna cewa akwai yara fiye da miliyan 87 a duniya da ke aikin karfi ko aikatau, kuma sun fi yawa ne a arewaci da kuma yammacin Afrika.

Arewacin Najeriya na daga cikin wuraren da wannan matsalar ke karuwa a cikin ƴan shekarun nan.

Bincike ya gano cewa matsalolin cin zarafin da yara kanana ke fuskanta na dakushe musu rayuwa, da janyo musu tsangwama a cikin al’uma da sauran su.

Kungiyar ba da agajin ta Save the Children ta ce tana bakin kokarinta wajen ganin an magance matsalolin, da tabbatar ganin an tallafawa wadanda suka samu kan su cikin irin wannan halin domin inganta rayuwarsu, da kwato musu hakkinsu idan bukatar hakan ta taso.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo da Hotuna,Wannan Matashiyar ta bayar da mamaki bayan da aka ganta da makudan kudade

Yaya girman matsalar yake a Najeriyar?

A cewar Hajiya Hafsat Baba, shugabar wata kungiyar kare haƙƙin mata da kuma kananan yara da ake kira Global Initiative for Women and Children a Najeriyar, kullum mastalar na ƙaruwa musamman a arewacin kasar, kuma lamarin ya shi shafar yaran da basu kai shekaru goma sha takwas ba.

Ta ce ire-iren cin zarafin na faruwa ne a gidaje, da makarantu, da wuraren aiki, da kuma wuraren da ake fama da yake-yake, da afkuwar bala’oin da suka shafi muhalli.

A cewarta ”Mafi akasarin yaran mata da ake kai su gidaje don yin aikatau ana ba su aikin da ya fi karfinsu, ba tare da ana biyansu albashi mai kyau ba, inda galibi abun da ake biyansun bai wuce Naira dubu hudu ba, domin ana fakewa da ana basu ci da sha da wurin kwana”

Karanta Wannan  Subhanallahi: Kalli Bidiyon wani dan Najeriya dake ikirarin Babu Allah, ya kara da cewa baya son taimakon Allah

“Akwai kuma kananan yara maza waɗan da ake turo su almajirci, amma sai ka ga malamansu na bautar da su ta hanyar kai su gona don su yi masu aiki” in ji ta.

Ta ƙara da cewa duk da cewar akwai dokar da aka samar ta kare haƙƙin yara a Najeriya matsalar na daɗa ƙaruwa.

Mece ce Mafita?

A wani mataki na kare hakkin irin waɗannan yara da ake azabtarwa dai, Majalisar Dattawan Najeriyar a watan Mayun shekarar nan ta 2024 ta fara wani yunkuri na kafa wata hukuma da za ta rika tattara bayanan ‘yan aikin da kuma iyayen gidansu.

Majalisar ta ce za a samar da hukumar ne domin tabbatar da kare ‘yan aiki wadanda a ko da yaushe suke fuskantar cin zarafi daga wajen iyayen gidansu.

Karanta Wannan  Hoto: An daure wannan mutumin saboda ya cire kwaroron roba yayin da yake jima'i da wata mata da suka amince cewa zai yi amfani da kwaroron roba amma ya yaudareta ya cire bata sani ba

Masu fafutuka sun yi maraba da wannan yunkuri, inda suke ganin zai matukar rage cin zarafin da ake yi wa ‘yan aiki.

Sai dai a cewar Hajiya Hafsa, idan ba a yi tsayin daka ba, babu wani sauyi da za a samu.

Kungiyar kwadago ta duniya ta ce cikin ‘yan aiki da ake da su a fadin duniya kashi 76 da digo biyu mata ne dalilin da ya sa cin zarafi ta hanyar fyade da kisan kai da kuma kin biyan albashi ya yawaita a bangaren mata ‘yan aiki ke nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *